IQNA

‘Yar Sanda Musulma A Holland Na Fuskantar Matsala Saboda Saka Lullubi

23:32 - October 20, 2017
Lambar Labari: 3482018
Bangaren kasa da kasa, wata yar sanda musulma a kasar Holland na fuskantar matsala sakamakon saka lullubi a kanta a lokacin aiki a kan haka ta kai kara.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, wata yar sanda musulma a kasar Holland na fuskantar matsala sakamakon saka lullubi a kanta a lokacin aiki, wanda hakan yasa ta kai kara domin a bi mata hakkinta.

Batul Auzatch Lauya mai kare wannan ‘yar sada ta bayyana cewa, wadda take karewa tana fuskantar matsain lamaba da takura daga hukumar ‘yan sanda ta kasar, bisa hujjar cewa saka hijabi a lokacin aikinta ya sabawa kaida domin ba aikin addini take yi ba.

Batul ta ci gaba da cewa, a halin yanz an shgar da kara a kan wannan batu, kuma tana fatan a yi adalci ga wadda take karewa, domin kuwa babu wata doka a cikin dokokin kasar Holland da ta hana mace ‘yar sanda ta saka lullubi a lokacin da take sanyeda kayan sarki.

Ta kara da cewa akwai wasu daga cikin manyan jami’an ‘yan sanda na kasar ne da suke son su yi amfan da hakan domin taye mata hakkinta, wanda kuma hakan ba daidai ba ne a shiga hakkin wata ‘yar kasa saboda addininta ko akidarta.

3654631


captcha