Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kungiyar ta Jihadul-Islami na yin Zanga-zanga a ranar juma'a 15 ga watan Decemba.
Kiran dai ya zo ne a daidai lokacin da al'ummar paladinu take ci gaba da gudanar da Zanga-zangar nuna kin amincewa da matsayar Amurka akan birnin kudus.
A gefe daya, sojojin haramtacciyar Kasar Isra'ila sun kai hare-hare akan yankuna daban-daban na palasdinu a lokacin da al'ummar Palasdinu ke gudanar da Zanga-zanga a garin Bethlehem da Isawiyyah.
Tun ranar laraba 6 ga watan Decemba ne dai shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin haramtacciyar Kasar Isra'ila.