Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya Asabar mambobi 15 na kwamitin tsaron MDD suka fara gudanar da bincike a game da koken da kasar Masar ta gabatar na watsi da sabon matakin da shugaban kasar Amurka ya dauka na ayyana birnin Qudus a matsayin hedkwatar Haramtacciyar kasar Isra'ila.
Rahoton ya ce akwai yiwuwar cewa a ranar Litinin ko Talata na wannan mako da muke ciki, za a kada kuri'ar watsi da wannan kuduri, duk kuwa da cewa kudirin nada magoya baya a tsakanin manbobin kwamitin tsaron MDD, kuma akwai yiwuwar Amurka ta hau kujerar naki a game da wannan kudiri.
Cikin koken da Masar ta gabatar, duk wani kudiri da zai canza yanayin birnin Qudus da al'ummarsa, ba shi da wani tasiri a hukumance, kuma bisa dokokin MDD wajibi ne ayi watsi da shi,sannan kuma an bukaci kasashen duniya da su kauracewa matakin Amurka na mayar da Ofishin jakadancinsu a Haramtacciyar kasar Isra'ila zuwa birnin Qudus.
A ranar 6 ga watan Disamba da muke ciki ne, duk da irin adawar da kasashen Duniya suka nuna, Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ayyana Birnin Qudus a matsayin hedkwatar Haramtacciyar kasar Isra'ila tare da bada umarnin dauke ofishin jakadancin kasarsa daga birnin Tel-Aviv domin mayar da shi zuwa birnin Qudus.