IQNA

Ana Kokarin Ganin An Sako Mata 13 Daga Gidan Kason Bahrain

23:14 - March 10, 2018
Lambar Labari: 3482464
Bangaren kasa da kasa, wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama na kokarin ganin an sani wasu mata da ake tsare da su a kurkukun masarautar Bahrain.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Lu’ulu’a cewa, yanzu wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama na kokarin ganin an sani wasu mata da ake tsare da su a kurkukun masarautar Bahrain da ake tsare da su saboda dalilai na siyasa.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan mataki ya zo bayan samun bayanai dangane da irin yadda matan suke fusknatr tsanani da cin zarafi daga masu tsaron gidan kason na masarautar kama karya ta kasar Bahrain.

A cikin bayanin da gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya suka fitar, da hakan ya hada hard a Amnesty International da kuma Human Rights Wach, ya tabbatar da cewa masarautar kasar Bahrain tana cin zarafin fararen hula masu saboda ra’ayoyinsu na siyasa, da ke neman a yi mulki na adalci a kasar mai makon kama karya.

Masarautar kasar tana yin amfani da karfi tare da taimakon manyan kasashen duniya musamman amurka da Birtaniya, da kuma wasu ‘yan korensu na yankin wajen murkushe ‘yan adawar siyasa.

3698407

 

 

 

 

captcha