Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Arab yaum cewa, a jiya an fara gudanar da gasar kur’ani da sunnar annabi (SAW) ta kasa da kasa a birnin Jakarta fadar mulkin kasar Indonesia tare da halartar wakilai daga kasashe 25 na duniya.
Wannan gasa za ta mayar da hankalia bangarori biyar ne, da suka hada da bangaren karau, da kuma hardar kur’ani, sai kuma bangaren hadisan manzon Allah (SAW.
Daga karshe za a bayar da kyautuka ga mutane uku da daya da na biyu da na uku a dukkanin bangarorin gasar, daga cikin yautukan da za a bayar ga wadanda suka zo na daya har zuwa aikin hajjin bana.