IQNA

Gasar Hardar Hudubobin Fatima Zahra (SA) A Madina

17:45 - March 23, 2018
Lambar Labari: 3482501
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da gasar hardar hudubobin Sayyida Fatima Zahra amincin Allah ya tabbata a gare ta a masallacin manzon (SAW) a Madina.

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa, cibiyar Zainab (SA) da ke karkashin kulawar hubbaren Imam Hussain (AS) ce ta dauki nauyin shira wannan gasa wadda ta kebanci mata zalla, inda matan da suka shiga gasar sun kai 200 a masallacin ma'aiki, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka.

Baya ga birnin Madina mai alfarma, an gudanar da wannan gasa a wasu birane na kasar Saudiyya, da nufin kara fadada lamarin manzon Allah da iyansa masu tsarki.

A shekarar da ta gabata ma an gudanar da irin wannan gasa, inda fiye da mutane 2800 daga kasar Iraki da suke ziyara suka shiga gasar.

3701678

 

captcha