Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Reauters cewa, mutumin da ya aikata wannan lamari ya kasha wani mutum a kusa da garin Trebes, kuma ya sace motarsa ya gudu.
Mutumin wanda ya bayyana kansa a matayin dan kungiyar ta’addanci ta Daesh, ya yi garkuwa da mutane a wani dakin cin abinci, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwa mutane biyu a wurin.
Emanuel Macron ya bayyana lamarin da cewa aiki ne na ta’addanci kuma yana da matukar hadari.
Daga bisani jami’an ‘yan sanda sun kashe mutumin tare da kubutar da mutanen da ya yi garkuwa da su.
Mutumin dai ya bukaci da a saki Salah Abdulsalam, mutumin da ake zargi da kai harin birnin Paris a cikin sekara ta 2015, wanda za a fara shari’arsa nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.