IQNA

An Bude Gasar Kur'ani Ta Duniya A Kasar Masar A Yau Asabar

17:21 - March 24, 2018
Lambar Labari: 3482505
Bangaren kasa da kasa, a yau Asabar an bude babbar gasar kur'ani ta duniya a kasar Masar tare da halartar daruruwan makaranta daga kasashen duniya hamsin.

 

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Sadal Balad ya habarta cewa, an bude gasar kur'ani ta duniya karo na ashirin da biyar a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar, wadda ma'aikatar kula da harkokin ta kasar ta dauki nauyin shiryawa.

Ministan ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar masar Muhammad Mukhtar Juma'a ne ya jagoranci taron bude gasar a yau.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wurin, ministan ya bayyana cewa, babbar manufar shirya gasar dai shi ne yada lamarin kur'ani, kuma a wannan lokaci ya zama wajibi su yi amfani da wannan damar wajen kara wayar da kai ga matasa musulomi wajen yin amfani da kur'ani domin yada sahihiyar fahimtar musulunci, sabanin yadda wasu suke yin amfani da hakan wajn bata sunan musulunci a duniya.

Gasar za ta ci gaba da gudana har zuwa ranar Alhamis mai zuwa, inda za a kammala ta tare da bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo a gasar.

3701856

 

 

 

 

captcha