IQNA

Kudurori 5 Na UNHRC Da Ke Zargin Isra'ila Da Take Hakkokin Palastinawa

17:24 - March 24, 2018
Lambar Labari: 3482506
Bangaren kasa da kasa, a zaman da kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya gudanar na shekara-shekara, ya amince da wasu kudurori guda biyar da suke zargin Isra'ila da take hakkokin Palastinawa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a zaman kwamitin an amince da cewa dole ne a kafa kasar Palastinu mai cin gishin kanta, tare da yin tir da abin da Isra'ila ke yi na kawo cikas ga wannan lamari.

Haka nan kuma da matakan da ta ke dauka na fitar da Palastinawa daga yankunansu tare da gina gina matsugunnan yahudawa 'yan share wuri zauna a cikin yankunan na Palastinawa na shekara ta 1976.

Dangane da batun tuddan Golan kuwa, kwamitin kare hakkin bil adama ya bayyana abin da Isra'ila take na mamaye yankin da kuma gina matsunnan yahudawa da cewa baya  akan kaida da doka.

Daga karshe kwamitin ya bukaci Isra'ila da ta zama mai girmama dokokin kasa da kasa, tare da mayar da dukkanin hakkokin Palastinawa da ta handame.

3701846

 

 

 

 

captcha