IQNA

Kasar Faransa Ta Shiga Cikin Kasashe Da Kyamar Musulmi Ke Karuwa

17:31 - March 24, 2018
Lambar Labari: 3482507
Bangaren kasa da kasa, wata kididdiga ta nuna cewa kyamar musulmi a kasar Faransa na karuwa fiye da kowane lokaci.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa jaridar Hurriat ta habarta cewa, wata kididdiga ta nuna cewa kyamar musulmi a kasar Faransa na karuwa fiye idan aka kwatanta da lokutan baya.

Jaridar Le Monde ta kasar Faransa ta bayar da rahoton cewa, kwamitin koli na kare hakkin bil adama  kasar Faransa ya fitar da rahotonsa na shekara-shekara da ke nuna cewa, kyamar musumi ta karua  kasar da kasha 7.5 cikin dari.

Wani jin ra'ayin jama'a ya nuna cewa, kasha 44 cikin dari na mutanen Faransa, suna kallon musulunci a matsayin wata babbar barazana ga kasarsu da kuma makomar tarihinta, yayin da kashi 61 suke ganin cewa saka hijabi yana a matsayin babban cikas ga lamurran rayuwa kuam zai kawo matsala ga Faransa.

Musulmin kasar dai adadinsu ya kai miliyan 5 zuwa 6, kuma adadin yana ci gaba da karuwa.

3701830

 

captcha