Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,a a zantawar da ya yi da tashar ala’am, Albukhaiti daya daga cikin manyan jagrorin kungiyar Ansarullah ya bayyana cewa, dakarun kasar Yemen da mayakn sa kai na kabilun larabawa sun hana dakarun kawancen Saudiyya isa filin jirgin Hudaidah a yunkurin da ‘yan mamaya suke yi na kwace iko da shi.
Yanzu haka dai kasashen duniya musamman na turawa da yahudawan sahyuniya suke taimaka ma Saudiyya a yakin da take kaddamarwa kan al’ummar musulmi na kasar Yemen.