IQNA

Na’ibin Limamin Tehran:

Halin Da Juyin Musulunci Ke Ciki Ya Kama Da Lokacin Yakin Ahzab

23:52 - June 22, 2018
Lambar Labari: 3482778
Bangaren siyasa, wanda ya jagoranci sallar juma'ar birnin Tehran ya bayyana cewar babu abin da takunkumin da Amurka ta sanya wa Iran zai haifar mata da kuma shi kansa shugaban kasar face kara kunyata su a idon duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidi Kermani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma'a a yau din nan a masallacin juma'ar birnin Tehran, inda yayin da yake ishara da kokarin da ma'abota girman kan duniya karkashin jagorancin Amurka suke yi wajen cutar da juyin juya halin Musulunci na kasar Iran ya bayyana cewar: Sakamakon takunkumin da Amurka ta sanya wa Iran zai zamanto abin kunya da kara bakanta sunanta da kuma shugaban kasar ne a idon duniya.

Na'ibin limamin Juma'ar na Tehran ya ci gaba da cewa: Babu wani abin da Amurka take kokarin yi face tabbatar da bakaken manufofinta, don haka ya kirayi al'ummar Iran da sauran al'ummomin Yankin Gabas ta tsakiya da su yi taka tsantsan da makirce-makircen ma'abota girman kan.

Har ila yau Ayatullah Kermani ya ce duk da ci gaba da danyen aikin da Amurka da kawayenta suke yi a kan kasashen yankin nan kama daga Yemen da Palastinu da sauransu, amma hakan ba zai hana kawo karshensu ba.

3724451

 

 

captcha