IQNA

Jerin Gwano Tunawa Da Shahadar Imam Hussain (AS) A Austria

23:40 - September 15, 2018
Lambar Labari: 3482985
Bangaren kasa da kasa, a yau Asabar an gudanar da babban gangami da jerin gwano a birnin Vienna na kasar Austria domin tunawa da shahadar Imam Hussain (AS).

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau Asabar 15 ga watan Satumban 2018, cibiyar Imam Ali (AS) ta shirya gudanar da babban gangami da jerin gwano a birnin Vienna fadar mulkin kasar Austria domin tunawa da shahadar Imam Hussain (AS) a cikin wannan wata.

A yayin gangamin an yi ta rera taken adalci ga musulmi da kuma kin jinin ayyukan wuce gona da iri da ta’addanci da ake dangantawa da musulmi.

Haka nan kuma an gabatar da jawabaia  wurin gangamin, dangane da rayuwar Imam Hussain (AS) da kuma iyalan gidan manzon Allah (SAW) da rin darussan da za a iya koyo daga rayuwarsu mai albarka.

A kowace shekara wannan cibiya tana daukar nauyin shirya tarukan Tasu’a da Ashura inda muuslmi mazauna birnin Vienna sukan halarta, kamar yadda baki daga kasashe daban da suka hada da Iran, Iraki, Turkiya, Afghanista Pakistan da dai sauransu duk suna halarta.

3746964

 

 

 

 

 

captcha