IQNA

Harin Ta’addanci Ya Lamukume Rayukan Mutane 12 A Afghanistan

23:26 - December 12, 2018
Lambar Labari: 3483211
Rahotanni daga kasar Afghanistan sun bayyana cewar adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon harin kunar bakin waken da aka kai wa jami'an tsaron kasar a wajen birnin Kabul, babban birnin kasar a yau Talata ya kai mutane 12.

Kamfanin dillancin labaran iqna, mataimakin kakakin ma'aikatar harkokin cikin gidan  kasar ta Afghanistan Nasrat Rahimi yana fadin cewa mutane 12,  jami'an tsaron guda hudu da wasu fararen hula su 8 ne suka rasa  rayukansu sakamakon harin kunar bakin waken.

Majiyoyin tsaron kasar Afghanistan din sun bayyana cewar an kai harin ne da wata mota da aka makare ta da bama-bamai a gundumar Paghman da ke yammacin birnin na Kabul a daidai lokacin da tawagar jami'an tsaron take dawowa daga wani sintiri na cikin dare.

Cikin 'yan shekarun nan dai jami'an tsaron Afghanistan din suna ci gaba da fuskantar hare-haren ta'addanci daga wajen 'yan kungiyar Taliban ta kasar inda a watan Nuwamban da ya gabata shugaban kasar Ashraf Ghani ya bayyana cewar kimanin sojoji da 'yan sandan kasar dubu talatin ne aka kashe tun daga shekara ta 2015 sakamakon irin wadannan hare-hare. 

 

3771783

 

 

 

captcha