Kamfanin dillancin labaran iqna, a gobe Lahadi en idan Allah ya kai mu za a kaddamar da sabon bugun littafin tafsiri mai suna tafsir Shams a ofishin kamfanin dillancin labaran iqna, tare da halartar babban malamin addini Ayatollah Sayyid Mustafa Mohaqqiq Damad.
Baya ga haka kuma taron kaddamar da wannan tafsiri zai samu halartar malamai na addini da kuma masana da masu nazari daga jami'oi na kasar Iran.
Taron zai gudana ne a babban dakin daruka na kamfanin dillancin labaran IQNA da ke birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran.
Kaddamar da wannan tafsiri zai kasance a daidai wannan rana ne da ake gudanar da tarukan tunawa da zagayowar lokacin haihuwar Imam Hassan Askari (AS).