IQNA

Australia Ta Amince Da Birnin Quds A Matsayin Fadar Mulkin Isra’ila

23:55 - December 15, 2018
Lambar Labari: 3483219
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Australia ta sanar da amincewa da birnin Quds a matsayin fadar mulkin Isra’ila  a hukumance.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya bada rahoton cewa, firayi ministan Australia Scott Jhon Morison ya  sanar da cewa, kasar ta amince da birnin Quds a matsayin  fadar mulkin Isra’ila.

Ya ci gaba da cewa, duk da cewa kasarsa ta amince da birnin Quds a matsayin fadar mulkin Isra'ila, amma kuma a halin yanzu ba su da wani shiri na dauke ofishin jakadancinsu daga Tel aviv zuwa birnin na Quds.

Kasar Australia dai na daga cikin kasashe masu bin siyasar Amurka ido rufe, kuma wannan matakin na zuwa ne bayan da gwamnatin Amurka karkashin shugabancin Donald Trump ta fara amincewa da birnin Quds a matsayin fadar mulkin Isra'ila, tare da dauke ofishin jakadancinta daga Tel aviv zuwa birnin Quds, lamarin da kasashen duniya suka yi Allawadai da shi, da hakan ya hada har da kasashen yammacin turai masu kawance da Amurka.

 

3772327

 

 

 

 

 

 

captcha