IQNA

An Yi Rijistar Sunayen Marayu Dubu 30 A Damascus

22:14 - December 16, 2018
Lambar Labari: 3483223
Bangaren kasa da kasa, ministar ayyuka da kula da harkokin zamantakewa a Syria ta ce an yi rijistar marayua kimanin dubu 30 a Damascus da kewaye.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau ministar ayyuka da kula da harkokin zamantakewa a Syria, ta sanar da cewa sun yi rijistar sunayen marayua kimanin dubu 30 a cikin birnin Damascus da kewaye wadanda iyayensu suka rasu sakamakon ayyukan ta’addanci.

Ta ce sun fara gudanar da wannan aiki tun a kwanakin baya, da nufin tantance adadin yara da iyayensu suka rasa rayukansu sakamakon ayyukan ta’addanci a kasar, inda aka fara ajiye yara 600 a gidan marayu, amma daga bisani adadin ya ci gaba da karu, inda ya nzu ya kai kimanin dubu talatin.

Ta ce za su ci gaba da gudanar da wannan aiki domin tabbatar da cewa an gano dukkanin marayu a kasar domin daukar nauyin rayuwarsu.

Wannan mataki na zuwa ne bayan gagarumar nasarar da gwamnatin Syria ta samu ne na murkushe ‘yan ta’addan wahabiyawan takfir da suka shelata yaki kan kasar tare da taimakon wasu sarakunan larabawa da kuma wasu kasashen yammacin turai da nufin kifar da gwamnatin Syria.

3773014

 

 

captcha