IQNA

Turkiya Ta Ce Saudiyya Bat Ta Bayar Da Hadin Kai Kan Batun Kisan Khashoggi

23:47 - December 17, 2018
Lambar Labari: 3483226
Ministan harkokin wajen kasar Turkiya Ahmad Jawish Auglo ya zargi gwamnatin kasar Saudiyya da kin bayar da hadin kai a binciken da bangaren shari'a na kasar Turkiya ke gudanarwa kan batun kisan Jamal Khashoggi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Shafin yada labarai na Khaleejonline ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabi a jiya  agaban taron Doha a kasar Qatar, Ministan harkokin wajen kasar Turkiya Ahmad Jawish Auglo ya bayyana cewa, Turkiya ta mika dukkanin bayanan da take da su dangane da kisan gillar da aka yi wa Jamal Khashoggi ga gwamnatin Saudiyya, amma har yanzu gwamnatin ta Saudiyya taki ta ce wa Turkiya uffan kan dukkanin bayanan da aka gabtar mata

Haka nan kuma ministan na Turkiya ya zargi kasashen turai da nuna halin ko in kula kan batun kisan gillar da k ayi wa Khashoggi, inda ya ce Turkiya ta mika sautin da aka nada  alokacin da jami'an tsaron Saudiyya suke yi wa Khashoggi kisan gilla a cikin ofishin jakadancin an Saudiya da ke Istanbul, amma har yanzu wadannan kasashen babu abin da suka yi kan batun.

Wannan furuci na ministan harkokin wajen Turkiya dai na zuwa ne bayan kudirin da majalisar dattijan Amurka ta amince da shi, wanda ya dora alhakin kisan Khashogi  a kan yariman Saudiyya mai jiran gado a Saudiyya Muhammad Bin Salman, inda 'yan majalisar dattijan na Amurka suka kafa hujja da bayanan da hukumar leken asirin ta Amurka CIA ta samu, da suke tabbatar da cewa Muhammad Bin Salman ne ya bayar da umarnin kisan Khashoggi, wanda hakan ya kawo baraka tsakanin majalisa da kuma shugaban na Amurka Donald Trump, wanda yake kare siyasar Saudiyya ido rufe.

 

3772935

 

 

 

 

captcha