IQNA

An Fara Gasar Kur”ani Ta Kasar Masar

23:49 - March 24, 2019
Lambar Labari: 3483486
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar kur’ani mai ta kasa da kasa a kasar Masar tare da halartar kasashe 60 na duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ministan ma’ikatar kula da harkokin addini a Masar Mukhtar Ali juma’a ya bayyana a wajen bude gasar cewa, kasashen Afrika 30 ne daga cikin kasashe 60 suke halartar gasar kur’ani mai tsarki ta duniya a kasar Masar ya zuwa yanzu haka.

Wanann gasar Kur’ani dai ana gudanar da ita ne a yankin Jizah daya daga cikin yankuna da ake mayar da hankali matuka ga hardar kur’ani mai tsarkia  kasar ta Masar.

Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka baki sun hallara domin halartar gsar wadda za ta kasance irinta ta farko da ke gudana a wanann yanki.

Cibiyar kula da harkokin kur’ani ta kasar masar karkashin ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ce ke daukar nauyin shirya gasar.

Mahardata da makaranta sittin ne za su kara da juna  a wannan gasa, inda za a gudanar da gasar a bangarori na harda da tilawa da kuma hukunce-hukuncen karatun kur’ani mai tsarki, kamar dai yadda bayanin ya ambata.

3799521

 

 

 

 

 

captcha