IQNA

Musulmin Amurka Za Su Dauki Nauyin Kare Wurarensu Na Ibada

23:51 - March 24, 2019
Lambar Labari: 3483487
Musulmin kasar Amurka suna shirin fara aiwatar da wani tsari na bayar da kariya ga masallatai da sauran wurarensu an ibada.

kamfanin dillancin labaran iqna, Shafin yada labarai na Dunya Bullteni ya bayar da rahoton cewa, a  cikin wani bayani da babbar cibiyar musulmi a birnin New na kasar Amurka ta fitar, ta bayyana cewa akwai daruruwan musulmi da suke da shirin fara gudanar da wani tsari na bayar da kariya ga wurarensu na ibada, da hakan ya hada da masallatai da kuma cibiyoyi gami da makarantu.

Bayanin ya ce yanzu haka an fara aiwatar da shirin a yankin Brooklyn da ke cikin gundumar New York, kuma yana gudana cikin nasara, a kan haka akwai yiwuwar za a aiwatar da irin wannan tsari a sauran jihohin kasar.

Wannan shiri dai yana gudana ne tare da kyakkyawan hadin gwiwa tsakanin musulmi da maam jami’an tsaro na kasar ta Amurka, sakamakon barazanar da musulmin suke fuskanta daga masu kyamar musulunci.

 

 

3799599

 

 

 

 

 

captcha