IQNA

Jami’an Tsaron Iraki Sun Rusa Sansanonin Daesh A Gundumar Karkuk

23:20 - March 25, 2019
Lambar Labari: 3483491
Rahotanni daga kasar Iraki na cewa, a jiya jami’an tsaron kasar sun samau nasarar ragargaza wasu sansanonin ‘yan ta’addan daesh guda a cikin Lardin karkuk.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Shafin yada labarai na Mashhad Al-arabi daga kasar Iraki ya bayar da rahoton cewa, a jiya rundunar hadin gwiwa mai yaki da ta’addanci a Iraki, ta samu nasarar kaddamar da wani farmaki a kan wasu amnyan sansanonin ‘yan ta’addan Daesh guda hudu da suka ragea  cikin Lardin Karkuk, kuma an tarwatsa dukkanin sansanonin.

Jami’an tsaron sun ce sun samu tarin makamai a wurin, da kuma abubuwa masu fashewa wadanda akae harhada bama-bamai das u, wadanda ‘ya’yan kungiyar suka rika yin amfani das u wajen kai hare-harea  cikin kasar ta Iraki.

A cikin farkon watan Disamban 2017 ne Firayi ministan Iraki na lokacin Haidar abadi ya sanar da kawo karshen kungiyar daesha  hukumance, duk kuwa da cewa an rusa daular kungiyar ne, amma akwai sauran mayakanta da suka warwatsu a cikin sassa na kasar.

 

3799624

 

 

 

 

 

captcha