IQNA

Musulmi Na Azumi A Cikin Dokar Zaman Gida A Wasu Kasashen Turai

23:53 - April 25, 2021
Lambar Labari: 3485845
Tehran (IQNA) sakamakon karuwar cutar korona a kasar Jamus Italiya da Faransa, musulmi suna azumi a karkashin dokar zaman gida.

A rahoton kamfanin dillancin labaran iqna, sakamakon karuwar cutar corona a kasar Jamus Italiya da Faransa, musulmi suna azumi a karkashin dokar zaman gida domin kaucewa yaduwar cutar.

 

Duk da cewa an sassauta dokar zaman gida a wasu kasashen wadda aka kafa a baya-bayan saboda karuwar yaduwar cutar corona, amma duk da haka a kan kayyade lokuta da mutane da za su iya gudanar da harkokinsu.

Musulmi Na Azumi A Cikin Dokar Zaman Gida A Wasu Kasashen Turai

A kasar faransa an kafa dokar cewa, dole ne daga karfe 7 na yamma kowa ya koma gida, wanda hakan yasa musulmi ba za su iya gudanar da sallolinsu da suke yi a masallatai ba, kamar yadda suka saba yia  kowace shekara, musamman ma sallar asham da ake yi bayan sallar Isha'i a masallatai da dama.

Musulmi Na Azumi A Cikin Dokar Zaman Gida A Wasu Kasashen Turai

A kasar Italiya kuwa musulmi sun samar da wani tsari ne na taimako, musamman wadanda suke da hali da suke daukar nauyin buda baki a masallatai da cibiyoyin addini, inda suke bayar da taimakon kai tsaye ga mutane domin su yi buda baki a gidajensu.

Musulmi Na Azumi A Cikin Dokar Zaman Gida A Wasu Kasashen Turai

3965686

 

 

captcha