A wani rahoto da shafin yada labaraiu na Alwafd ya bayar, cibiyar da ke sanya ido kan lamurran musulmi a duniya da ke karkashin cibiyar Azhar da ke Masar ta sanar da cewa, bisa ga rahotanni da hukumomin tsaro suke fitarwa a Najeriya, a cikin lokutan baya-bayan nan satar mutane tare da yin garkuwa da su yana kara kamari a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa, mafi muni a cikin lamarin shi ne yadda masu aikata wannan mummunan laifin suke sace yara ‘yan makaranta tare da yin garkuwa da su da cutar da su, wanda hakan yana sanya fargaba matuka dangane da makomar lamurran tsaro a Najeriya, wanda tabbas zai cutar da harkar ilimi a kasar.
Haka nan kuma bayanin cibiyar ya yi ishara da cewa, wajibi ne day a rataya kan hukumomin Najeriya su kara zage dantse su yi kamar suna yi, domin ganin sun tunkari wannan mummunan aiki da bata gari suke yia kasar, haka nan kuma su kara matsa kaimi wajen tunkarar yaduwar ta’addanci da sunan addini ko jihadi a kasar.