IQNA

Qadir Akaras: Juyin Da Imam Khomeini Ya Jagoranta Juyi Ne Na Dukkanin Al’ummomi Raunana

18:47 - June 03, 2021
Lambar Labari: 3485977
Tehran (IQNA) shugaban cibiyar Alkauthar a Turkiya ya bayyana cewa, juyin da marigayi Imam Khomeini ya jagoranta juyi ne na dukkanin raunana.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ya gabatar dangane da cikar shekaru 32 da rasuwar marigayi Imam Khomeini, shugaban cibiyar Alkauthar a Turkiya Qadir Akaras ya bayyana cewa, juyin juya halin muslunci da marigayi Imam Khomeini ya jagoranta, juyi ne na dukkanin raunana a duniya.

Ya ce, abin da marigayi Imam Khomeini ya yi, ya tabbatar da cewa shi yana tare da taimakon Allah ne, domin kuwa abu ne wanda babu wanda ya taba zaton cewa haka za ta yiwu, musamman ganin cewa gwamnatin Iran a  wancan lokacin tana dasawa ne da dukkanin manyan kasashen duniya ‘yan mulkin mallaka, kuma su ne suke ba ta kariya.

Amma duk da haka tare da taimakon Allah, malami mai tsoron Allah da tasbaha a hannunsa, ya jagoranci al’ummarsa wajen kawar da wannan gwamnati ta zalunci da danniya, ya kuma tabbatar da tsari na adalci da daidaito tsakanin al’ummarsa, tare da kawo karshen biyayya ido rufe da Iran take yi wa kasashen turai da yahudawa a wancan lokacin, wanda kuma babban abin day a jawowa kasar matsananciyar kiyayya daga wadannan kasashe tun daga lokacin wannan juyi.

Malamin ya ci gaba da cewa, juyin da marigayi Imam ya yi, ya wayar da al’ummomin duniya da dama, musamman ma raunana daga cikinsu, wajen mikewa tare da kin amincewa da zalunci da danniya da mamaya ta kasashe ‘yan mulkin mallaka masu girman kai.

Akaras ya kara da cewa, wannan ba lamari ne da zai iya faruwa cikin sauki ba, za  aiya cewa idan ba tare da taimakon Allah ba, hakan ba abu ne mai yiwuwa ba, wanda kuma daga nan masu hankali da ilimi da basira za sui ya gane matsayin mutumin da Allah ya ba shi wannan taimako.

Dangane da yanayin rayuwar marigayi Imam Khomeini kuwa, Qadir Akaras ya bayyana cewa, dukkanin rayuwarsa abin koyi ce ga kowa, domin kuwa mutum ne wanda abin duniya bai dame shi ba, yana a matsayin jagora na kasa kamar Iran, amma ya rasu bai mallaki gida na kashin kansa ba, sai dai a gidan haya ya rayu har ya rasu, bai mallaki wani abin hawa ba balantana sauran kayan alatu na rayuwa, in banda tulin littafai babu abin da ya mallaka a rayuwarsa.

3975391

 

 

captcha