IQNA

Kafa Kawancen Gwagwarmaya A Gabas Ta Tsakiya Sakamako Ne Na Juyin Da Imam Khomeini Ya Yi

23:55 - June 04, 2021
Lambar Labari: 3485984
Tehran (IQNA) shugaban mabiya mazhabar Ahlul bait (AS) a Bahrain ya bayyana kafuwar kawancen gwagwarmaya da cewa sakamako ne na juyin Imam Khomeini a Iran.

Shugaban mabiya mazhabar Ahlul bait (AS) a Bahrain Ayatollah Sheikh Isa Qasem ya bayyana cewa,  kafuwar kawancen gwagwarmaya a yankin gabas ta tsakiya, sakamako ne na juyin juya halin muslunci da marigayi Imam Khomeini ya jagoranta.

Shehin malamin ya bayyana hakan ne a yau a lokacin da yake gabatar da jawabia  wurin taron tunawa da cikar shekaru 32 da rasuwar marigayi Imam Khomeini, inda aka watsa jawabin nasa ta hanyar hoton bidiyo a yanar gizo a kan manyan alluna na talabijin.

Ayatollah Isa Qasem ya yi ishara da cewa, kafin yunkurin Imam Khomeini, yankin gabas ta tsakiya ya zama yanki ne da turawa 'yan mulkin mallaka suke cin karensu babu babbaka, kuma babu wanda ya isa ya ce da su uffan.

Amma bayan tabbatar da juyin juya halin da ya yi a kasar Iran, hakan yasa komai ya sauya a yankin, inda hatta al'ummar Falastinu sun samu karfin gwiwa wajen mikewa domin su kwaci hakkokinsu da aka haramta musu.

Baya ga haka kuma kungiyoyin gwagwarmaya da mulkin mallaka  da mamaya ta kasashe masu girman kai a yankin gabas ta tsakiya sun ci gaba da bullowa, inda a halin yanzu su ne suka hana kasashe masu girman kai cimma burinsu a yankin.

Wannan kuma bai tsaya a nan ba, domin kuwa tunani irin na Imam Khomeini na son kafa adalci da kwato hakkokin raunana, ya isa ko'ina a duniya.

3975345

 

captcha