IQNA

MDD Ta Bukaci A Kara Yawan Taimakon Da Ake Kai Wa Ga Al’ummar Yankin Gaza

14:43 - June 10, 2021
Lambar Labari: 3486000
Tehran (IQNA) ofishin majalisar dinkin duniya a yankin zirin Gaza ya sanar da cewa ana fusakantar matsalolin rayuwa masu yawa a yankin.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da ofishin majalisar dinkin duniya a yankin zirin Gaza ya bayar, ana fusakantar matsaloli masu yawa a yankin, sakamakon karancin shigar da kayayyakin bukatar rayuwa.

Babbar jami’ar majalisar dinkin duniya mai kula da ayyukan agaji a Gaza Lynn Hastings ta bayyana cewa, a halin yanzu akwai bukatar fitar da dubban mutane daga yankin domin yi musu magani a asibitocin kasashen waje.

Ta ce daga cikinsu akwai wadanda suka samu munanan raunuka sakamkaon hare-haren Isra’ila, baya ga haka kuma akwai wadanda suke da matsaloli na musamman, kamar masu fama da cutar daji wato cancer, da kuma masu wasu cututtukan da ke bukatar fitar da su waje, amma har yanzu Isra’ila tana kawo cikas da tarnaki wajen gudanar da wadannan ayyuka.

Baya ga haka kuma babbar jami’ar ta majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa, kashi 50% na kayayakin bukatar rayuwa da ake shigar da su a Gaza, ana shigar da su ne ta mashigar Abulkaram, wanda Isra’ila ta rufe wanann mashigar, tare da kayyade abubuwan da za a iya wucewa da su, wanda hakan yasa abubuwa da dama na bukatar rayuwa ba za a iya shiga da su yankin Zirin Gaza ba.

 

3976572

 

 

captcha