IQNA

An Raba Kwafin Kur'ani miliyan 1 Da Aka Tarjama A Cikin Harsuna 10 A Saudiyya

23:01 - June 12, 2021
Lambar Labari: 3486005
Tehran (IQNA) an raba kwafin kur'ani miliyan daya da aka tarjama a cikin harsuna 10 ga cibiyoyin addini 413 domin rabawa ga mutane.

Jaridar Makka ta bayar da rahoton cewa, bisa umarnin sarkin Saudiyya Salman Bin Abdulaziz, ministan kula da harkokin addini a kasar ta saudiyya ya raba kwafin kur'ani miliyan daya da aka tarjama a cikin harsuna 10 ga cibiyoyin addini 413 domin rabawa ga mutane a ciki da wajen kasar.

Abdullaitif Al Sheikh shi ne ministan ma'aikatar kula da harkokin addini, shi ne kuma shugaban madaba'antar sarki Fahad da ke buga littafai da kwafi-kwafi na kur'ani mai tsarki, ya bayyana cewa, wannan aikin raba kur'anai ya zo ne bayan umarnin da sarki Salman ya bayar kan hakan.

Ya ci gaba da cewa, babbar manufar hakan ita ce yada koyarwa irin ta kur'ani a tsakanin al'ummomi wadanda suke fahimtar larabci da ma wadanda ba su fahimta, wanda hakan ne dalilin tarjama kur'ani zuwa harsuna daban-daban na duniya.

 

3976836

 

 

captcha