IQNA

Kotun Bahrain Ta Tabbabatar Da hukuncin Dauri Shekaru 5 Kan Nabil Rajab

23:53 - December 31, 2018
Lambar Labari: 3483270
Bangaren kasa da kasa,bayan sanar da wannan hukunci,  kotun masarautar kama karya ta kasar Bahrain ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 5 a gidan kaso kan shugaban cibiyar kare hakkin bil adama na kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a nata bangaren Kungiyar ta kare hakkib bil'adama ta kasa da kasa ta ce; hukuncin ci gaba da tsare Nabil Rajab, babban abin kunya ne.

A bayanin da kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta fitar a yau Litinin ta ce; Daurin wasu karin shekaru biyar da aka yi wa mai fafutukar kare hakkin dan'adam Nabil Rajab, take adalci ne kuma abin kunya

Kungiyar ta kira yi gwamnatin kasar Bahrain da ta soke hukuncin ba tare da wani sharadi ba

Tun a ranar sha uku  ga watan Yuni na dubu biyu da sha shida ne dai jami'an tsaron kasar Bahrain su ka kame Nabil Rajab wanda shi ne shugaban cibiyar kare hakkin bil'adama, saboda wata hira ta talabijin da ya yi.

Tun wancan lokacin har zuwa yanzu ana ci gaba da tsare da shi. 

A yau Litinin ne wata kotu a kasar ta Bahrain ta yanke masa hukuncin zaman kurkuku na tsawon shekaru biyar

Kasar Bahrain ta fada cikin dambaruwar siyasa ne tun a cikin watan Febrairu na dubu biyu da sha daya saboda yunkurin al'ummar kasar na son ganin an kafa tsarin demokradiyya.

3777198

 

 

 

 

captcha