IQNA

Kungiyiyon Falastinawa SunJadddaAzamar Ci Gaba Da Gwagwarmaya

23:55 - May 15, 2020
Lambar Labari: 3484800
Tehran (IQNA)dukkanin kungiyoyin sun jadadda wajabcin ci gaba da gwagwarmayarhar zuwa karshen mamayar kasarsu ta 1948 da Isra’ila ke yi.

Kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa sun jaddada cewar ba za su taba amincewa da wani abu ko wani waje a matsayin kasarsu in ba Palastinu ba, haƙƙin komawar ‘yan gudun hijira Palastinawa kasarsu ta Palastinu kuwa wani haƙƙi ne da su yi watsi da shi ba.

Kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawan sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da suka fitar a yau din nan Juma’a don tunawa da ranar Nakbah, ranar da aka kafa haramtacciyar kasar Isra’ila inda suka yi watsi da batun da ake yi na zaunar da Palastinawa ‘yan gudun hijira a wasu kasashe na duniya maimakon dawowa kasarsu ta asali wato Palastinu, inda suka ce ba za su taɓa amincewa da wata ƙasa a matsayin makwafin Palastinu ba.

Har ila yau ƙungiyar gwagwarmayar Palastinawan sun sake jaddada hakkin da al’ummar Palastinu suke da shi na gwagwarmaya da neman haƙƙoƙinsu ta dukkanin hanyoyin da suka sawwaka musu ciki kuwa har da gwagwarmaya ta makami, suna masu cewa za su ci gaba da bin tafarkin da suka riƙa har sai sun kwato hakkokinsu daga wajen yahudawan sahyoniya ‘yan share guri zauna.

Yau Juma’a 15 ga watan Mayu yayi daidai da zagayowar shekaru 72 na ranar Nakbah wato ranar da aka kafa haramtacciyar ƙasar Isra’ila a shekarar 1948 a ƙasar Palastinu sakamakon makirci ƙasashen yammaci musamman Birtaniyya.

 

3899032

 

captcha