IQNA

Falastinawa Sun Fatattaki Wasu Larabawan Bahrain Da UAE Masu Yawon Shakawata A Isra’ila

23:41 - December 20, 2020
Lambar Labari: 3485476
Tehran (IQNA) Falastinawa sun nuna fushinsu a  kan wasu larabawan Bahrain da UAE da suka ziyarci Isra’ila domin yawon shakatawa.

Jaridar ra’yul yaum ta bayar rahoton cewa, larabawan wadanda suka shiga cikin yankunan Falastinawa da visa ta Isra’ila, sun gamu da fushin al’ummar Falastinu, inda ake jefe su da takalma da kuma yi musu eho a duk inda suka shiga cikin yankunan Falastinawa.

Rahoton ya ce, larabawan na Bahrain da UAE sun shiga cikin harabar masallacin Quds, amma masu kula da masallacin suka hana su shiga, daga karshe dai sun shiga masallacin mai alfarma ta kofar da yahudawa suke shiga

Wani daga cikin yahudawa masu tsatsauran ra’ayi ya bayyana wa tashar talabijin ta 11 ta Isra’ila cewa, ya yi mamakin yadda Falastinawa suka hana larabawan Bahrain da na UAE shiga cikin masallacin quds, wanda hakan ke nuni da cewa Falastinawa ba su yarda da kulla alaka da Isra’ila da gwamnatocin wadannan kasashe suka yi ba.

Ya kara da cewa, yahudawa ne suka baiwa larabawan ‘yan yawan shakatawa a Isra’ila kariya, domin kare su daga abin da ka iya faruwa da su, sakamakon fushin da Falastinawa suka nuna dangane da zuwan nasu karkashin Bakuncin yahudawan Isra’ila.

3942159

 

 

 

captcha