IQNA

MDD: Yunwa Za Ta Iya Halaka Miliyoyin Mutane A Yemen Matukar Ba A Dauki Mataki Ba

21:59 - January 12, 2021
Lambar Labari: 3485549
Tehran Majalisar dinkin duniya ta bayar da rahoton cewa, akwai babbar barazanar yunwa da ke a kasar Yemen, da ke bukatar daukar matakin gaggawa.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, mai magana da yawun hukumar bayar da agaji ta majalisar dinkin duniya Vanessa Huguenin ta bayyana cewa, bisa ga sakamakon binciken da aka gudanar, a halin yanzu kimanin mutane miliyan 13.5 ne suke cikin mawuyacin hali na yunwa da rashin abincin da za su ci.

A nata bangaren hukumar abinci ta majalisar dinkin duniya FAO ta sanar da cewa, mai yiwuwa daga nan zuwa watan Yuni na wannan shekara ta 2021, mutane miliyan uku za su akan adadin da aka ambata, wanda hakan ke nufin cewa fiye da rabin mutanen kasar Yemen za su fada cikin matsananciyar yuwa.

Bayanin ya ce nauyi ne da ya rataya kan al’ummomin duniya da su taimaka wajen fitar da al’ummar Yemen daga cikin wannan mawuyacin hali, wanda rashin samun wani dauki dauki zai yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a cikin wannan shekara saboda yunwa.

Al’ummar kasar Yemen ta fada cikin wannan mawuyacin hali ne tun bayan da gwamnatin kasar Saudiyya ta fara kaddamar da hare-hare kan al’ummar kasar shekaru shida da suka gabata, da sunan yaki da kungiyar Huthi da ba ta dasawa da bangarorin da Saudiyya ke mara wa baya a Yemen.

3947331

 

captcha