IQNA

Amsar Babban Shehin Azhar Ga Yahudawa Kan Da’awar Da Suke Yi Dangane Da Masallacin Quds

17:33 - May 20, 2021
Lambar Labari: 3485933
Tehran (IQNA) Babban malamin cibiyar ilimi ta Azhar a kasar Masar ya bai wa yahudawan sahyuniya amsa ka da’awar da suke yi dangane da masallacin Quds.

Shafin yada labarai na jaridar Al-naba ya bayar da rahoton cewa, Sheikh Ahmad Tayyib ya bayar da amsa dangane da da’awar da yahudawa suke yi a kan masallacin Quds mai alfarma, inda ya ce shi ne wuri na biyu mai albarka da aka gina a bayan kasa domin shiryar da dan adam.

Ya ce Annabi Adamu (AS) ne ya gina wannan masallaci shekaru arba’in bayan ya kammala aikin ginin dakin Ka’abah.

Sheikhul Azhar ya bayyana cewa, ya zo a cikin ruwayar Abu Zar Algifari (RA) yana cewa; na tambayi manzon Allah (SAW) cewa wane masallaci ne aka fara ginawa a bayan kasa, sai ya ce; masallacin Harami (Ka’abah) sai na ce daga shi kuma sai wane? Sai ya ce; masallacin Aqsa, sai na ce; shekaru nawa ne tsakanin ginin masallatan biyu? Sai ya ce; shekaru 40.

Malamin ya ci gaba da cewa; yahudawa sun dauka cewa Annabi Dawud (AS) da Annabi Sulaiman (AS) ne suka gina masallacin Aqsa, alhali wannan tunanin asu kure, domin kuwa Annabi Dawud (AS) da Annabi Sulaiman (AS) sun gyara wani bangare ne na masallacin wanda ya rushe.

 

3972684

 

 

captcha