Mehdi Gholamnejad, makarancin kur'ani mai tsarki na kasarmu, ya karanta ayoyi 40 zuwa 47 na suratul Hud da kuma Suratul Kauthar a rana ta biyu ta gasar kur'ani mai tsarki ta duniya karo na 40 da kuma gasar daliban kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa karo na 8 da aka gudanar a dakin taro na Tehran.