IQNA

Majalisar Dinkin Duniya Ta Jaddada Wajabcin kawo Karshen Killace Gaza

23:48 - May 01, 2015
Lambar Labari: 3239038
Bangaren kasa da kasa, majalisar dinkin duniya ta jaddada wajabcin kawo karshen killace yankin zirin Gaza da haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na AFP cewa, Nikolay Maladonov manzon musamman na majalisar dinkin duniya da ke shiga tsakani a gabas ta tsakiya ya jaddada wajabcin kawo karshen killace yankin zirin Gaza da haramtacciyar kasar Isra’ila ke yin a tsawon shekaru.
Jami’in na majalisar dinkin duniya ya ci gaba da cewa a nasu bangaren palastinawa ya zama wajibi su mayar da hankali ga batun hadin kai a tsakaninsu, domin samun damar warware matsal;olin da ke tsakaninsu da Isra’ila, domin rashin hadin kan da ke tsakaninsu shi ne babban karfen kafa na dukkanin matsalolin da ke fuskanta.
Haka nan kuma ya kirayi sauran kasashe da su taimaka wajen ganin an samu sulhu da zaman lafiya mai dorewa  atsakanin palastinawa da kuma Israila, tare da kiranta ita da ta bayar da hadin kai domin ganin an cimma wannan burin a samu zaman lafiya a tsakaninsu.
A cikin shekara ta 2014 ne dai kungiyoyin Fatah da kuma Hasam suka rattaba hannu na kafa gwamnatin hadin kan kasa da za ta hada dukaknin bangarorin palastinawa, da nufin dunke dukaknin barakar siyasa da ke tsakaninsu, domin tunkarar manufa guda ta kafa kasar Palastinu.
3237947

Abubuwan Da Ya Shafa: mdd
captcha