IQNA

Hussain Ruyavaran:

Yarjejeniyar Karni Hadari Mafi Girma Ga Palastine

23:49 - May 28, 2019
Lambar Labari: 3483680
Yanzu haka dai Amurka da Isra’ila gami da wasu daga cikin kasashen larabawa suna shirin aiwatar da abin da ake kira da yarjejeniyar karni kan batun Palastine.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Hussain Ruyavaran masani kan harkokin Palastine ya bayyana cewa, Ita dai wannan yarjejeniya wadda Amurka da Isra’ila ce suka kirkiro ta, kuma suka umarci wasu daga cikin sarakunan larabawa masu yi musu biyayya sau da kafa, kan su dauki nauyin aiwatar da ita, wanda kuma a wannan shekara ranar Quds ta duniya da Imam Khomaini (RA) ya assa za ta mayar da hankali domin kalubalntar wannan yarjejeniya.

A halin yanzu dai Amurka da Isra’ila sun umarci Bahrain da ta dauki nauyin bakuncin taron tabbatar da wanann yarjejeniya, tare da aikewa da goron gayyata zuwa ga sauran kasashe, daga ciki har da wadanda su ne suka shirya lamarin wato Amurka da Isra’ila, gami da Saudiyya da Masar da kuma Jordan.

Yanzu haka dai an aike da goron gayyata zuwa ga kasashe da dama domin halartar taron, daga ciki kuwa har da gwamnatin Isra’ila da kuma gwamnatin kwarya-kwaryan cin gishin kai ta Palastine, to sai gwamnatin Falastinawan ta ce ba za ta halarci wannan taro ba.

Kasashen da suka shirya wannan abin da suke kira da yarjejeniyar karni, suna bayyana hakan a matsayin wata yarjejeniya wadda za ta kawo karshen rikci tsakanin Isra’ila da Falastinawa a jimlace.

To sai dai abin yake zahiri sabanin haka ne, domin a cikin yarjejeniyar babu inda aka ambaci kafa kasar Palastine mai cin gishin kanta a kan iyakokin Palastine da majalaisar dinkin duniya ta shata.

Haka nan kuma yarjejeniyar tana kunshe da wasu abubuwa masu hadari ga makomar Palastine da al’ummarta baki daya, da hakan ya hada da haramta wa miliyoyin falastinawa da suke gudun hijira a kasashen ketare dawowa kasarsu, tare da halasta mamayar birnin Quds da kuma amincewa da shi a matsayin babban birnin Isra’ila, kamar yadda kuma yarjejeniyar za ta halasta wa Isra’ila mallakar dukkanin yankunan Falastinawa da ta mamaye.

Wannan ya sanya dukkanin al’ummar Palastine bakinsu ya zo daya wajen yin watsi da wannan yarjejeniya, wadda suke kallonta a matsayin wani sabon salon yaudara da ke nufin mayar da su karkashin mulkin mallakar Isra’ila a hukumance.

A cikin ‘yan makonnin da suka gabata, tahsar almayadin ta nakalto daga wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin palastine cewa, gwamnatin Saudiyya ta yi wa shugaban Falastinawa tayin kudade hard a biliyan goma domin ya amince da wannan yarjejeniya, ama yaki amincewa da hakan, inda yake ganin amincewa da wannan yarjejeniya na a matsayin cin amana ne ga al’ummar Falastine da ma larabawa baki daya.

 

 

3814940

 

captcha