IQNA

An Bukaci Gudanar da Bincike Kan Harbin Karamin Yaro Da Isra’ila Ta Yi

23:50 - July 31, 2019
Lambar Labari: 3483899
Bangaren kasa da kasa, kwamitin kare hakkin bil adama na MDD ya bukaci a gudanar da bicike kan harbin wani yaro da sojojin Isra’ila suka yi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shugaban kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya bayyana damuwa kan halin da Abdulrahman Al-shawi yak e ciki.

Ya ce wannan dan shekaru 9 da haihuwa baya a matsayin wata barazana ga Isra’la, amma jami’an tsaro sun harbe shi da harsasai masu rai a garin Nablus.

Jami’in y ce suna bukatar ganin an gudanar da bincike na gaskiya kana bin da ya faru da wannan yaro, kuma a dauki matakai na hukunta wadanda suka aikata hakan.

A jiya ce sojojin Isra’ila suka bude wuta kan wannan karamin yaroa  garin Nablus a lokacin da wasu matasa suke wani jerin gwanoa  lokacin da yke tsayea  gefen titi, a halin yanzu yana nan rai kwakwai mutu kwakwai.

 

3831416

 

captcha