Kamfanin dillancin labaran WAFA ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ya gabatar a yau, wanda kafofin yada labaran Palestine suka watsa kai tsaye, Shugaban Falastinawa Mahmud Abbas ya bayyana cewa, ba za su taba yarda da shirin Isra’ila na yunkurin mamaye wasu sabbin yankuna na falastinawa gabar yamma da kogin Jordan ba.
Ya ce suna da cikakkiyar masaniya kan dukkanin abin da yake faruwa dangane da wannan shiri da Isra’ila take da shi, kuma take da niyyar aiwatar da shi tare da taimakon gwamnatin Amurka.
Mahmud Abbas ya ce yakin da suke yi da cutar corona ba zai hana su yaki da manufofin mamaya na Isra’ila ba, a kan haka yana kira tun wuri Amurka da Isra’ila da su sake tunani kan hakan.