IQNA

Zanga-zangar adawa da wariyar launin fata da kyamar musulunci a birnin Paris

16:12 - April 23, 2024
Lambar Labari: 3491030
IQNA - Babban birnin kasar Faransa ya shaida gagarumar zanga-zangar nuna adawa da wariya da kyamar Musulunci, wadanda aka gudanar saboda yakin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anatoly na birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa cewa, an gudanar da zanga-zangar nuna adawa da wariya da kyamar musulmi da cin zarafin kananan yara bayan samun izinin shari’a.

Dubban masu zanga-zangar ne suka yi ta rera taken nuna adawa da wariyar launin fata da 'yan sanda a Faransa.

Masu zanga-zangar sun kuma daga tutocin Falasdinawa da tutoci masu dauke da taken "A daina wariyar launin fata", "A daina kyamar Musulunci", "Ya'yanmu na cikin hadari" da kuma "A kawo karshen kisan kiyashi a Gaza".

Sakamakon tashe-tashen hankulan da yakin yahudawan sahyoniya ya haifar a zirin Gaza, wanda ya shafe sama da watanni 6 ana gwabzawa, a watannin da suka gabata ne aka sake shawarta matakin haramta zanga-zanga a Faransa.

Hukumomin Faransa sun ce sun haramta zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu da dama a cikin kasar mai dimbin al'ummar Musulmi da Yahudawa, a kokarinta na hana aikata laifukan kyama da tashe-tashen hankula masu alaka da kyamar Yahudawa.

A ranar Lahadin da ta gabata, masu zanga-zangar sun gudanar da wani tattaki na lumana daga unguwar Barbes da ke da yawan kabilu zuwa dandalin Jamhuriyar, inda da dama suka yi ta rera wakokin tunawa da wani yaro dan Arewacin Afirka (Nael) mai shekaru 17 da 'yan sandan Faransa suka kashe.

Shi ma shugaban ‘yan sandan birnin Paris Laurent Nunez ya shaida wa gidan talabijin na BFM cewa tun da farko an yanke shawarar hana tafiyar; Domin masu shirya taron sun kwatanta tashin hankalin 'yan sandan Faransa da yakin Gaza, kuma saboda haka taron na iya yin barazana ga zaman lafiyar jama'a.

Duk da haka, Kotun Gudanarwa ta Paris ta yi watsi da wannan hujja a cikin gaggawar yanke shawara.

Daya daga cikin wadanda suka shirya tattakin ya yi maraba da hukuncin kotun kuma ya lura cewa: Gwagwarmayar mutane da haduwa don tallafa wa dukkan yara abu ne na halitta kuma wajibi ne.

برگزاری تظاهرات علیه نژادپرستی و اسلام‌هراسی در پاریس + عکس

برگزاری تظاهرات علیه نژادپرستی و اسلام‌هراسی در پاریس + عکس

برگزاری تظاهرات علیه نژادپرستی و اسلام‌هراسی در پاریس + عکس

 

4211865

 

 

 

 

captcha