Tun kafin wannan lokacin an shirya wannan daftarin kudiri da nufin kada kuri'a a kansa a majalisar Knesset, amma saboda wasu dalilai aka dakatar da kada kuri'ar, wanda ahalin yanzu Netanyahu da mukarrabansa za su gabatar da shi, wanda kuma ake sa ran zai samu amincewar 'yan majalisar masu tsatsauran ra'ayi da ke mara baya ga Netanyahu.
Kasashen larabawa da na msuulmi da dama sun yi Allawada da wannan daftarin kudiri, tare da bayyana shi a matsayin daya daga cikin hanyoyin cin zarafin palastinawa musulmi, wasu daga cikin majami'oin mabiya addinin kirista da ke cikin yankunan Palastinawa da Isra'ila ta mamaye, sun rika saka kiran sallar asuba, domin nuna goyon bayansu ga musulmi.