IQNA

Netanyahu Ya Ce A Ci Gaba Da Tsaurara Bincike A Kan Palastinwa A Quds

21:59 - July 26, 2017
Lambar Labari: 3481739
Bangaren kasa da kasa, Firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila Benyamin Netanyahu ya bayar da umarni ga jami'an tsaron yahudawan Isra'ila da su gaba da tsaurara bincike a kan Palastinawa a birnin Quds da kuma masallacin Aqsa mai alfarma.

Kamfanin dilalncin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, Tashar talabijin ta almayadeen ta bayar da rahoton cewa, bayan dakatar da bincike a kofofin lantarki a masallacin aqsa, firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila Benyamin Netanyahu ya bayar da umarni ga jami'an tsaron yahudawan Isra'ila da su gaba da tsaurara bincike a kan Palastinawa a birnin Quds da kuma masallacin Aqsa mai alfarma ta hanyar yin amfani da kayan bincike na hannu.

Kafin wannan lokacin da jami'an tsaron yahudawan Isra'ila tare da umarnin Netanyahu sun kafa kofofin bincike na karfe masu aiki da lantarki a kan dukkanin hanyoyin da ke isa cikin harabar masallacin Aqsa mai alfarma, matakin da ya fuskanci kakakusar suka da Allah wadai daga kasashen duniya, da suka hada har da wasu kasashen turai, lamarin da ya tilasta Netanyahu bayar da umarnin janye wadannan kofofi.

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa jami'an tsaron yahudawan Isra'ila sun kai wani farmakia safiyar yau a wani sansanin Palastinawa da ke gabashin birnin Quds, inda suka dauki ba dadi da matasan palastinawa.

3623362


captcha