IQNA

Tsokacin Kafofin Yada Labarai Kan 'Yar Takara Musulma A Arizona

21:53 - August 01, 2017
Lambar Labari: 3481757
Bangaren kasa da kasa,a karon farko wata musulma ta tsaya takarar neman kujerar asanata a kasar Amurka daga jahar Arizona.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa unews cewa, Didar Abbud musulma 'yar takarar neman kujera a majalisar dattijan Amurka daga jahar Arizona karkashin inuwar jam'iyyar Democrat ta mayar da martini dangane da sukar ta da wasu ke a shafukan yanar gizo.

Didar ta bayyana cewa a matsayin na 'yar kasar Amurka mai cikakken 'yanci tana da hakkin tsayawa takara, wannan kuma shi ne 'yanci na demokradiyya, saboda haka babu abin da za ta boye dangane da addinta ko akidarta.

Ta ci gaba da cewa abin da ke da muhimamnci shi ne yin aiki bisa abin da dimukradiyya ta ginu a kansa, tare da yin adalcia tsakanin 'yan kasa da yi musu bisa da kuma cika musu alkawali, amma addini ko akida kowa yana da nasa addini ko akida da ya yi imani da ita.

Kotun jahar Arizona ta yi jinjinawa wannan 'yar takara musulma, tare da bayyana kalamanta da cwa suna kan hanya, kuma hakan abin koyi ne ga duk dan kasa na gari.

3625546


captcha