IQNA

Wasu Sun Lakada Wa Wani Limamin masallaci Duka A Kasar Serbia

23:44 - March 27, 2018
Lambar Labari: 3482516
Bangaren kasa da kasa, wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun lakada wa wani limami duka a kasar Serbia.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, Salihovic shi ne limamin masallaci musulmi a garin Novi Pazar, wanda ya sha duka da zagi da cin zarafi daga wasu mutane.

Gamayyar kungiyoyin musulmi a kasar Serbia ta fitar da bayani da ke cewa, sakamakon duka da aka yi wa malamin, ya samu munanan raunuka a jikinsa.

Jami'an tsaro sun ce har yanzu ba su kame kowa kan lamarin ba, amma dai suna gudanar da bincike domin sanin wadanda suke da hannu wajen aikata wannan aika-aika.

Wannan dai ba shi ne karon farko da musulmi suke fuskantar irin wannan cin zarafi a kasar Serbia ba, kuma lamarin yana kara ta'azzara ne a cikin shekarun baya-bayan nan, sakamakon bullar kungiyoyi masu adawa da musulmi a kasar.

3702026

 

 

 

 

captcha