IQNA

Cibiyar Fatawa Ta Masar: Tsoron Kamuwa Da Corona Ba Zai Hana Azumi Ba

23:43 - April 16, 2020
Lambar Labari: 3484716
Tehran (IQNA) babbar cibiyar bayar da fatawa ta kasar Masar ta sanar da cewa, yaduwar cutar corona ba zai hana daukar azumi ba.

Jaridar Yaum Sabi ta kasar Masar ta bayar da rahoton cewa, babbar cibiyar bayar da fatawa ta kasar Masar Darul Ifta ta sanar da cewa, bayan tattaunawa da kwararrun likitoci, sun cimma matsaya kan cewa yaduwar cutar corona ba zai hana daukar azumi ba.

Bayanin ya ce ga likitoci da sauran jami’an kiwon lafiya da suke gudanar da aiki wajen yaki da corona, idan hakan zai iya cutar da su, bai kamata su dauki azumi ba.

Haka nan kuma wadanda suke fama da cutar corona, likitoci za su duba matsayin kamuwarsa da cutar da kuma matsayin azumi ga makomar lafiyarsa, abin da likitoci suka fadi ta fuskar kiwon lafiya dole ne a yi amfani da shi.

 

3891913

 

 

 

captcha