IQNA

Trump Ya Sanar Da Kulla Alaka Tsakanin Bahrain Da Isra’ila

23:45 - September 11, 2020
Lambar Labari: 3485171
Tehran (IQNA) Shugaban Amurka ya sanar da bude shafin alaka tsakanin masarautar Bahrain da kuma gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, a yau Juma’a Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da bude shafin alaka tsakanin masarautar Bahrain da kuma gwamnatin yahudawan Isra’ila.

A cikin wani bayani na hadin gwiwa da masarautar Bahrain tare da Amurka da kuma Isra’ila suka fitar, sun sanar da kulla alaka tsakanin gwamnatin ta Bahrain da kuma gwamnatin yahudawan Isar’ila.

A cikin shafinsa na twitter Trump ya sanar da cewa, a  yau an kara samun wani babban ci gaba ta fuskacin sulhu a gabas ta tsakiya, inda Bahrain ta bi sahun hadaddiyar daular larabawa wajen yin sulhu da Isra’ila tare da sanar da kulla alaka ta diflomasiya da ita.

Ita ma a nata bangaren gwamnatin yahudawan ta sana da cewa wannan bababn ci gaba ne a aka samu na diflamasiyya, wanda zai kara taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

Tun kafin wannan lokacin dai Amurka ta sanar da cewa wasu daga cikin kasashen larabawa za su sanar da kulla alaka da Isra’ila, inda hadaddiyar daular larabawa ta fara fitowa a fili ta sanar da kulla wannan alaka ‘yan kwanakin da suka gabata, sai kuma Bahrain a  yanzu.

Jamia’n Isra’ila sun bayyana cewa suna da kyayyawar alaka da wadannan kasashe tun fiye da shekaru ashirin da suka gabata, yanzu  ne dai alakar ta fara fitowa fili a hukumance.

3922280

 

captcha