IQNA

Morocco Ta Ce Ba Ta Taba Yanke Hulda Da Gwamnatin Yahudawan Isra'ila Ba

19:04 - December 14, 2020
Lambar Labari: 3485457
Tehran (IQNA) Gwamnatin kasar Morocco ta sanar da cewa, babu wani abu sabo dangane da alakarta da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

A cikin bayanin da gwamnatin kasar Morocco ta bayar dangane da kulla alakarta da Isra’ila, ta bayyana cewa abin da ya faru ba kulla alaka ba ne, ci gaban alaka ne tsakaninsu da Isra’ila, domin kuwa da can akwai alaka  a tsakaninsu.

Gwamnatin kasar Morocco ta bi sahun kasashe uku daga cikin kasashen larabawa da suka fito fili suka bayyana kulla alakarsu da gwamnatin yahudawan Isra’ila, inda a  halin yanzu ta zama ta hudu.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ne ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa ta sanya larabawa sun kulla alaka da Isra’ila a bayyane, domin hakan ya kara tabbatar da halscin Isra’ila da kuma samuwarta a yankin gabas ta tsakiya.

Ko a  cikin ‘yan makonin da suka gabata na gudanar da zaman tattaunawa tsakanin a cikin kasar saudiyya, tsakanin yarima mai jiran gado Muhammad Ben salman, da kuma sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo gami da firayi ministan gwamnatin yahudawan Isra’ila Benjamin Netanyu.

صلحی که جنگ جدیدی با خود خواهد آورد

Amus Jaled wanda shi ne babban jami’I mai kula da cibiyar bincike a bangaren ayyukan tsaro na Isra’ila, ya bayyana cewa kasashen Morocco da Sudan sun kulla alaka da Isra’ila ne ba tare da sun samu komai daga Isra’ila ba, domin dukkanin alkawullan da aka yi musu kan hakan tsakaninsu da Amurka ne.

Gwamnatin Trump ta yi Morocco alkawalin cewa, idan ta fito ta sanar da kulla alaka da Isra’ila a bayyane, to kuwa Amurka za ta amince da ikon Morocco a kan yankin Sahara.

صلحی که جنگ جدیدی با خود خواهد آورد

Sai dai kasar Aljeriya ta bayyana matakin na Morocco da cewa babban kure ta tafka, domin kuwa alkawalin da Amurka ta yi mata ba zai iya tabbatar da ikonta  akan yankin Sahara ba.

Kungiyoyin farar hula da jam’iyyun siyasa a cikin kasar suna ci gaba da yin tir da Allawadai da wannan mataki da gwamnatin kasar ta dauka, tare da bayyana cewa ba da sunan al’ummar kasar ne gwamnatin Morocco ta kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila ba.

 

3940800

 

captcha