IQNA

Bahrain Da Isra’ila Sun Janye wa Juna Visa Ga Jami’an Diflomasiyya

22:53 - January 28, 2021
Lambar Labari: 3485597
Tehran (IQNA) Bahrain da Isra’ila sun janye wa juna izinin shiga kasashen juna daga yau ga jami’an diflomasiyya.

Ma’ikatar harkokin wajen kasar Bahrain ta sanar da cewa, sun cimma matsaya tare da bangaren Isra’ila da Italiya Hungry kan janye izinin shiga cikin kasashen juna daga wannan rana ga jami’an diflomasiyyarsu.

Wannan shiri yana daga cikin abubuwan da gwamatin Bahrain da kuma gwamnatin yahudawan Isra’ila suka cimma matsaya a kansu tun alokutan baya, lokacin da suka kulla alaka a tsakaninsu.

Haka nan kuma wannan yana a matsayin mataki na farko ne, amma gwamnatin Bahrain tana niyayr kara fadada wannan matsaya ta yadda za ta janye izinin shiga ga yahudawan Isra’ila domin shiga cikin kasar Bahraina  duk lokacin da suka ga dama.

Amurka ta taka gagarumar rawa wajen kara hada alaka tsakanin gwamnatin yahudawan Isra’ila da kuma wasu gwamnatocin larabawa da suka hada da Bahrain.

 

3950474

 

captcha