IQNA

Afirka Ta Kudu: Hada-Hadar Kudade Bisa Tsarin Musulunci Na Samun Karbuwa Cikin Sauri

23:03 - May 22, 2021
Lambar Labari: 3485937
Tehran (IQNA) Harkokin mu’amalar kudade bisa tsarin muslunci na samun karbuwa a kasar Afirka ta kudu.

Shafin yada labarai na Pak Observer ya bayar da rahoton cewa, cibiyar da ke kula da harkokin mu’amalar bankuna  a kasar Afirka ta kudu BASA ta sanar da cewa, mu’amalar kudade bisa tsarin muslunci na samun karbuwa da ci gaba a kasar .

Bayanin ya ce; a cikin shekarar 2020, bankin da ke kula mu’amalar kudade bisa tsarin muslunci, kudinsa sun karu daga dalar miliyan 886.8, zuwa dala biliyan 1.04.

Na’im Ibrahim darakta na bangaren harkokin kasuwanci a bankin muslunci na FN a kasar Afirka ta kudu ya bayyana cewa, suna gudanar da harkokinsu ne bisa tsari wanda bai saba wa shari’ar muslunci ba.

Ya ce dukkanin wadanda suke mu’amala da wannan banki, bisa amincewa da dukkanin sharuddansa ne suke mu’amala da shi, wanda kuma hakan ya hada da musulmi da ma wadanda ba musulmi ba.

Ibrahim ya kara da cewa, bankin yana gudanar da harkokinsa ne kamar yadda kowane banki ke yi, amma akwai abubuwa wadanda ya kebanta da su da babu a sauran bankuna, kamar karbar riba ko bayarwa, da kuma yin kasuwanci a abubuwa da aka haramta a muslunci, kamar barasa, ko naman alade, da makamantan hakan.

 

3972782

 

captcha