IQNA

Hamas: Shirin Isra’ila Na Gina Sabbin Matsugunnan Yahudawa Dubu 3 A Falastinu Laifin Yaki Ne

15:00 - October 28, 2021
Lambar Labari: 3486485
Tehran (IQNA) Kungiyar Hamas ta mayar da martani kan shirin Isra’ila na gina matsugunnan yahudawa guda dubu uku a cikin yankunan Falastinawa.

Cibiyar yada labarai a Falastinu ta bayar da rahoton cewa, Kakakin kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas Hazim Kasim mayar da martani da kakkausar murya kan shirin Isra’ila na gina matsugunnan yahudawa guda dubu uku a cikin yankunan Falastinawa da ta mamaye a yamacin kogin Jordan.

Ya ce amincewar da gwamnatin yahudawan Isra’ila ta yi da shirin gina sabbin matsugunnai guda dubu uku a cikin yankunan Falastinawa, shi kansa wani laifi ne na yaki kara da take aikatawa a kan idon duniya, wanda ta cancancia  hukunta a kansa.

Kasim ya ce, abin da yake faruwa ya kara tabbatar wa Falastinawa da cewa, babu wata hanya ta shiryawa da Isra’ila illa daukar matakai na kariyar kai, da kuma kwatar hakkokinsu da ta mamaye ta hanyar gwagwarmaya.

Daga karshe ya kirayi al’ummomin duniya da su takawa gwamnatin yahudawan burki kan irin wannan ta’asa da take aikatawa kan al’ummar Falastinu.

4008649

 

captcha