IQNA

Rufe ofishin jakadancin yahudawan sahyoniya a Afirka ta Kudu

14:28 - November 22, 2023
Lambar Labari: 3490190
Johannesburg (IQNA) Majalisar dokokin Afirka ta Kudu ta kada kuri'ar rufe ofishin jakadancin yahudawan sahyoniya da ke kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sputnik cewa, majalisar dokokin kasar Afrika ta kudu ta kada kuri’ar amincewa da rufe ofishin jakadancin Isra’ila da ke kasar tare da katse huldar diflomasiyya, tare da nuna adawa da yadda al’amura ke ci gaba da tabarbarewa a Gaza.

Majalisar dokokin Afirka ta Kudu ta kuma kada kuri'ar dakatar da jakadan Isra'ila a kasar Afirka ta Kudu.

Kungiyar lauyoyin da ke da cibiya a Afirka ta Kudu ta kuma sanar da aiwatar da wannan hukunci har sai Isra'ila ta amince da tsagaita bude wuta a Gaza.

Kuri'ar dai ta biyo bayan tabarbarewar dangantakar da ke tsakanin Isra'ila da Afirka ta Kudu, kuma na zuwa ne bayan shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana irin ayyukan da Isra'ila ke yi a Gaza a matsayin kisan kare dangi.

Ma'aikatar harkokin wajen gwamnatin Sahayoniya ta sanar a shafinta na yanar gizo na "X" a ranar Litinin din da ta gabata cewa: Biyo bayan bayanan da Afirka ta Kudu ta yi a baya-bayan nan, an gayyaci jakadan Isra'ila a Pretoria don tuntubar juna.

A farkon wannan watan, Afirka ta Kudu ta kira jakadanta daga Isra'ila tare da janye dukkan jami'an diflomasiyya daga kasar.

Ya zuwa yanzu dai Isra'ila ta ki ba da sanarwar tsagaita bude wuta na jin kai a zirin Gaza duk da bukatu da dama na kasa da kasa; Yayin da mutuwa da barna suka dabaibaye Palasdinawa daga kowane bangare.

4183398

 

captcha