IQNA

Wata ‘yar sandan Amurka ta musulunta a wani masallaci a birnin New York

16:26 - April 28, 2024
Lambar Labari: 3491058
IQNA - Wata ‘yar sanda Ba’amurkiya  ta musulunta ta hanyar halartar wani masallaci a birnin New York.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yeni Shafaq al-Arabiya cewa, karuwar dabi’ar addinin muslunci a shekarun baya-bayan nan ya kasance daya daga cikin muhimman abubuwan da suka nuna yadda addini ya kasance a Amurka.

Da dama dai sun gabatar da addinin Musulunci a matsayin addini na farko wajen karuwar mabiya a Amurka, kuma da dama sun yi hasashen cewa nan da shekara ta 2040, Musulunci zai zarce addinin Yahudanci kuma ya zama addini na biyu a Amurka.

A shekarun baya-bayan nan dai an zargi Musulman Amurka da kara nuna kyama da kuma tuhume-tuhume daban-daban da suka hada da goyon bayan ta'addanci, sannan kuma sun sha kokawa kan yadda 'yan sanda da hukumomin tsaro ke nuna musu wariya musamman bayan abubuwan da suka faru a ranar 11 ga watan Satumba.

Bayan farmakin guguwar Al-Aqsa da kuma ayyana goyon bayan musulmi ga al'ummar Palastinu, wadannan zarge-zarge sun sake tasowa.

 

 

 

 

4212548/

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: musulunta addini musulunci amurka yahudanci
captcha